An fattaki Lakurawa daga Arewa Maso Yamma – Matawalle

17 hours ago 2

Karamin ministan tsaro, Hon. Bello Mohammed Matawalle, yace kawo yanzu sun kakkabe Lakurawa daga yankin Arewa Maso Yamma.

Ministan tsaron ya ce, dakarun sojoji sun hallaka gungun ‘yan ta’addan, sannan sun kuma tarwatsa sansanoninsu da kwato bindigogi da alburusai daga hannunsu.

Ya kuma ce “Mun gama da su a yankin Arewa maso yamma. Duk wanda ke batun cigaba da wanzuwar Lakurawa yana yi ne kawai domin ya bata kimar gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro”

Matawalle ya kuma kalubalanci alumma da su daina amincewa da irin wadannan ikirarin ba tare da tantance sahihancin bayanan ba.

An fattaki Lakurawa daga Arewa Maso Yamma – Matawalle

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.