Ana cinikin N50b duk mako a kasuwar shanu a Kano

11 hours ago 2

Shugaban riko na Kasuwar Shanu ta Wudil, Alhaji Ahmad Dauda, ya bayyana cewa kasuwar tana gudanar da hada-hadar kudi har Naira biliyan 50 a kowanne mako. A lokacin da ya ke magana da manema labarai a Kano ranar Talata, Alhaji Dauda ya bayyana cewa suna samun kudin daga shanun da suke sayarwa, kuma sun kan sayar da shanun da ba su kasa miliyan uku ba a kasuwar da ke gudana kowanne Juma’a da Asabar.

Ya bayyana cewa shanun ana kawo su ne daga Kano da wasu jihohi, ciki har da Adamawa, Bauchi, Plateau, Taraba, Sokoto, Borno, da Yobe. Mafi yawan dabbobin, a cewarsa, ana fitar da su zuwa yankunan Kudu-maso-Kudu, Kudu-maso-Gabas, da Kudu-maso-Yamma na Najeriya.

Kasuwar Wudil, wacce ita ce babbar kasuwar shanu a jihar Kano, tana daga cikin manyan kasuwanni a arewacin Najeriya, inda ake gudanar da hada-hadar kudi har Naira biliyan 50 a kowanne Juma’a. Shanun suna fara isa kasuwar daga ranar Laraba a tireloli da manyan motoci, sannan ana fara sayar da su daga ranar Juma’a zuwa Asabar.

Shugaban rikon ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa samar da kayayyakin more rayuwa da kasuwar ke bukata, ciki har da magudanan ruwa, fitilu masu amfani da hasken rana, da bandakuna. Sai dai, ya nuna damuwa kan matsalar ruwa, yana mai cewa akwai bukatar karin magudanan ruwa a kasuwar domin saukaka fitar ruwa, musamman a lokacin damina.

Alhaji Dauda ya kuma roki gwamnati da ta samar da ingantaccen tsaro a kasuwar, saboda akwai rahotannin satar dukiya daga hannun ‘yan kasuwa a baya, wanda ya sanya barazanar tsaro ta zama muhimmiyar bukata.

Ana cinikin N50b duk mako a kasuwar shanu a Kano

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.