Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya aika da ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi Umar, wadda ta rasu a ranar Laraba, 25 ga Disamba, 2024, bayan gajeruwar rashin lafiya.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Hon. Mati Ali, ya fitar a ranar Laraba, Ministan ya bayyana matukar jimami game da wannan babban rashi.
Ya ce: “Na samu labarin rasuwar Hajiya Maryam Namadi Umar, mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa, da tsananin damuwa da alhini. Wannan labari mai cike da bakin ciki ya girgizani matuka.”
Ministan ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga Gwamnan, iyalansa, da al’ummar Jihar Jigawa, yana mai bayyana rasuwar a matsayin babbar asara.
Ya yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama, ya sanya ta cikin Aljannar Firdausi, kuma ya baiwa iyalanta hakuri da karfin zuciya a wannan mawuyacin lokaci.
Ya ce: “Ina rokon Allah Madaukaki ya jikan ta da rahamarsa, ya ba iyalanta juriyar daukar wannan babban rashi.”
Badaru ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Jigawa bisa rasuwar mahaifiyarsa