Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), reshen Lagos, ta yabawa Matatar Dangote bisa saukar farashin mai da aka yi kwanan nan, tana mai bayyana wannan a matsayin taimako ga tattalin arzikin ’yan Najeriya a wannan lokaci na kunci.
Shugabar NLC ta jihar Lagos, Funmi Sessi, wacce ta yi wannan yabon cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ta ce zuwan Matatar Dangote a wannan lokaci ya na muhimmanci kwarai da gaske.
Sessi ta bayyana fatan cewa saukar farashin zai rage kudin sufuri, farashin kaya tare da bayar da rangwame ga ’yan Najeriya da ke fama da tsadar rayuwa.
“Wannan sauyin farashin ya kasance wani muhimmin taimako ga miliyoyin ’yan Najeriya da suka dade suna fama da tsadar mai da kuma tsadar rayuwa.
“Idan ba don matatar Dangote ba, muna ganin gwamnati na iya ci gaba da shigo da mai daga ƙasashen waje.
“Amma yanzu, Dangote na samar da kimanin ganguna 650,000 na mai a kowace rana, yayin da matatun mai na Fatakwal da wasu da aka gyara ke samar da kusan ganguna 210,000 a rana, wanda ba ya kai rabin abin da Dangote ke samarwa.
“Da wannan, Dangote ya kawo gasa mai kyau a cikin bangaren, kuma mun fara ganin raguwar farashin mai,” in ji ta.
Shugabar ta kuma lura cewa matatar Dangote ta fara fitar da mai zuwa kasashe kamar Ghana, Togo, da sauran su.
A cewarta, wannan yana nufin cewa za a samu dagawar darajar kudin kasar.
“A wannan lokaci, muna yaba wa Dangote. Muna kuma godiya bisa wannan matakin da ya dauka cikin lokaci.
“Kada kuma mu manta cewa Majalisar Dokoki ta Kasa tana kokarin fitar da kudiri da zai tilasta amfani da kudin Najeriya a cikin gida.
“Abin takaici ne cewa kudinmu ya rasa ƙarfinsa, har a yankin Yammacin Afirka.
“Don haka, ya kamata gwamnati ta karfafa wa Dangote da sauran masu zuba jari da ke shigowa don tabbatar da gasa mai kyau.
“Muna maraba da wannan rangwamen, wanda zai taimaka wa ’yan Najeriya da ke fama da tsadar rayuwa, kuma muna kira ga sauran masu ruwa da tsaki su kwaikwayi abin da Dangote ke yi don amfanin kowa,” in ji Sessi.