Fiye da Mutane 213 sun mutu a turmutsutsi a Najeriya cikin shekaru 11

3 hours ago 2

Fiye da mutane 213 sun rasa rayukansu sakamakon turmutsutsi daban-daban a Najeriya cikin shekaru 11 da suka gabata, kamar yadda bincike ya nuna.

Yawancin turmutsutsin faru ne yayin rabon kayan abinci, yayin da wasu suka faru a tarukan addini da gwajin daukar ma’aikata.

A cikin kwanaki shida da suka gabata kacal, turereniyar rabon kayan abinci ta hallaka mutane kusan 72 a Ibadan, Jihar Oyo; Okija, Jihar Anambra; da Abuja.

A ranar Laraba, yara kusan 40 ne suka rasa rayukansu yayin wata liyafa da tsohuwar Sarauniyar Ooni na Ife, Naomi Shikemi, ta shirya a Makarantar Sakandare ta Islamic High School da ke Bashorun, Ibadan.

Turereniyar Abuja da ta Anambra kuwa sun faru ne ranar Asabar. Rahotanni sun nuna cewa mutane 10 sun mutu a Abuja, yayin da 22 suka mutu a Anambra, tare da wasu da dama da suka jikkata.

A ranar 22 ga Maris, dalibai mata biyu na Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a turereniyar da ta faru yayin bikin yaye dalibai.

A ranar 15 ga Maris, 2014, mutane 16 sun mutu yayin turereniyar daukar ma’aikata ta Hukumar Shige da Fice (NIS).

Haka zalika, a ranar 2 ga Nuwamba, 2013, mutum 25 sun mutu, wasu 200 kuma suka jikkata a turereniyar da ta faru a Majami’ar Holy Ghost Adoration Ministry da ke Uke, Anambra.

A shekarar 2022, mutum 31 sun mutu a turereniyar rabon kayan abinci da aka shirya a Fatakwal, Jihar Ribas, yayin shirin Shop for Free na cocin King’s Assembly.

Fiye da Mutane 213 sun mutu a turmutsutsi a Najeriya cikin shekaru 11

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.