Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya amince da bayar da kyautar Kirsimeti ta naira 100,000 ga ma’aikata, ma’aikatan gwamnati, da kuma masu ritaya a jihar.
An sanar da wannan amincewar ne a wata sanarwa da shugaban ma’aikata na jihar, George Nweke, ya fitar a daren Talata kuma aka raba wa kafafen watsa labarai.
Nweke ya bayyana cewa wannan kyautar Kirsimeti an tsara ta domin taimakawa ma’aikata da sauran su wajen biyan buƙatun su na lokacin bikin Kirsimeti, kuma za a fara aiwatar da ita nan take.
Sanarwar ta ce: “Ina sanar da al’umma cewa Mai Girma Gwamna Siminalayi Fubara, a cikin farin cikin bikin Kirsimeti, ya amince da biyan naira 100,000 ga ma’aikatan gwamnati, da kuma masu ritaya a Jihar Rivers, domin su samu damar gudanar da bukin Kirsimeti cikin farin ciki.
“Mai Girma Gwamna ya amince da wannan kuduri a ranar Litinin, 23 ga Disamba, 2024, kuma ya umarci a fara aiwatar da shi nan take don tabbatar da cewa ma’aikatan sun yi bikin Kirsimeti cikin jin daɗi.”
George Nweke ya kara da cewa wannan shine karo na biyu a lokacin Gwamna Fubara da ma’aikatan gwamnati ke karɓar kyautar Kirsimeti ta naira 100,000, wadda ta zarce mafi ƙarancin albashi na kasa baki ɗaya. Haka kuma, wannan shi ne karo na farko da masu ritaya za su samu wannan tallafin.
Gwamna Fubara ya baiwa ma’aikata da masu ritaya kyautar kirsimeti ta N100,000