Gwamna Hyacinth ya yi alƙawarin binciko maharan ranar Kirsimeti

16 hours ago 2

Gwamnan jiihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana matuƙar alhini kan hare-haren da aka kai wa al’ummar Anwase a ƙaramar hukumar Kwande, inda ake zargin makiyaya sun kashe fiye da mutane goma da ke bikin Kirsimeti a ranar 25 ga Disamba.

Masu kai harin sun kuma auka wa wasu garuruwa a yankin, inda suka jikkata mutane da dama.

Yanzu haka, wasu daga cikin waɗanda suka ji rauni suna karɓar magani a asibitoci.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sir Kulas Tersoo, ya sanya wa hannu, kuma aka bai wa ‘yan jarida a ranar Juma’a, Gwamna Alia ya yi Allah wadai da harin.

Ya nuna takaicinsa kan ci gaba da faruwar irin waɗannan hare-hare duk da ƙoƙarin gwamnatinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamnan ya sake tabbatar da jajircewarsa wajen kare mutanen ji
Benue, tare da kira ga hukumomin tsaro da su ƙara sa ido da kare al’ummomin da ke cikin haɗari.

“Zan iya tabbatar muku, waɗanda suka aikata wannan aikin ba za su
tsira ba. Suna iya tunanin ba a san su ba, amma ba za a bari su ci gaba da aikata wannan ba. Magana ce ta lokaci,” in ji Gwamna Alia.

Haka kuma, ya miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da nuna juyayi ga waɗanda suka ji rauni, yana mai alkawarin ganin an hukunta waɗanda suka aikata wannan ta’asa.

Ƙaramar Hukumar Kwande, wacce ke iyaka da karamar hukumar Takum a Jihar Taraba kuma tana da iyaka ta ƙasa da yankin Kamaru ta Kudu, ta dade tana fama da rikice-rikice.

Gwamna Hyacinth ya yi alƙawarin binciko maharan ranar Kirsimeti

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.