Gwamna Otti yayi kira da a guji halaye masu haddasa hatsaniya

5 hours ago 1

Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya bukaci masu shirya tarukan da ke jan hankalin mutane da su tabbatar da daukar matakan tsaro masu inganci domin kaucewa mummunan hatsari kamar su turmutsutsi musamman a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

Gwamnan ya kuma gargadi mutane kan wasu halayen da ba su dace ba, kamar lika da watsa kudi ko kaya cikin taron jama’a, yana mai cewa irin wannan dabi’ar na iya haifar da hatsaniya da turereniya.

A cikin kalamansa, Gwamna Otti ya ce, “Duk wanda zai shirya taron da ke bukatar taron jama’a ya tuntubi Ma’aikatar Tsaron Gida ta Jihar Abia ko hukumomin kananan hukumomi domin samun shawarwari da tallafin da ya dace, don tabbatar da tsaron mahalarta taron.”

Haka kuma, Gwamnan ya jaddada cewa za a dauki tsauraran matakai kan duk wani mutum ko kungiya da sukayi watsi da wannan umarni.

Gwamna Otti yayi kira da a guji halaye masu haddasa hatsaniya

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.