Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa za ta fara gurfanar da duk masu ƙin biyan kuɗaɗen haraji a shekarar 2025.
Wannan ya zo ne a matsayin wani ɓangare na gyare-gyare da gwamnatin ke yi domin inganta tattara kuɗaɗen shiga.
Wannan batu na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, inda ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen tabbatar da bin dokokin haraji ba tare da ƙara sabon haraji ba.
A cewar shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta Jihar Kano (KIRS), Dr. Zaid Abubakar, “Gwamnati ba za ta ƙara haraji ba, amma zamu tabbatar da an bi doka wajen biyan kuɗaɗen haraji da kuma inganta hanyoyin tara su.”
Dr. Zaid ya bayyana wannan ne yayin da yake gabatar da jawabi ga Gwamnan Jihar a wajen wani taron bita da aka shirya don manyan jami’an gwamnati. Ya kuma bayyana hasashen hukumar KIRS na samun kuɗaɗe fiye da naira biliyan 20 a kowanne zango na shekarar 2025.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa gyare-gyaren da aka yi a hukumar tara haraji, wanda ya haɗa da sauke tsohon shugaban hukumar da naɗin sabo, sun taimaka sosai wajen ƙara samun nasarori a zangon uku da na huɗu na shekarar 2024.
Sanusi Bature ya ƙara da cewa: “Duk waɗannan matakan na da nufin tabbatar da cewa kuɗaɗen harajin jihar ba su salwanta ba kuma an yi amfani da su yadda ya dace.”
Gwamnatin Kano ta shirya gurfanar da masu kin biyan haraji daga 2025