Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun koyon aikin lafiya

14 hours ago 1

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun koyar da aikin lafiya masu zaman kansu a jihar da ba su da rajista.

Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin lafiya, Alhaji Umar Mamuda, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a ma’aikatar yada labarai da al’adu ta jihar Katsina.

Ya ce sakamakon binciken da ma’aikatar lafiya ta jihar ta gudanar kwanan nan ya nuna cewa akwai makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da dama da ba su cika ka’idoji ko samun rajista ba. Wannan, a cewarsa, na iya zama barazana ga lafiyar al’umma.

Hukuncin rufe makarantun zai ci gaba da aiki har sai an kammala tantancewa da kuma sake rajistar su. Alhaji Mamuda ya bukaci masu makarantun da abin ya shafa su garzaya ma’aikatar lafiya ta jihar domin tantancewa da karbar rajista.

Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun koyon aikin lafiya

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.