Gwamnatin tarayya ta ba da hutun karshen shekara

6 hours ago 3

Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba da Alhamis, da kuma 1 ga Janairu, 2025 a matsayin ranakun hutu a kasa baki daya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan ma’aikatar cikin gida, Dr. Magdalene Ajani, ta rattaba hannu a ranar Litinin a Abuja.

A cewar Ajani, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa hutun an tsara shi ne domin bai wa ‘yan kasa damar murnar bikin Kirsimeti, da kuma Boxing Day da ma Sabuwar Shekara.

Tunji-Ojo ya jaddada mahimmancin lokacin bikin a matsayin lokaci na karfafa zaman lafiya da ƙarfafa dangantaka tsakanin iyalai da al’umma.

Ya tabbatar wa ‘yan kasa cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da kuma wadata a duk fadin kasar.

Haka kuma, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan ajandar “sabuwar fata” na gwamnatin Shugaba Tinubu wajen tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a shekarar 2025.

Ministan, a madadin gwamnatin tarayya, ya aika sakon fatan alheri ga daukacin ‘yan Najeriya, yana kira da su yi amfani da wannan lokaci don bunkasa zaman lafiya, da hadin kai.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutun karshen shekara

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.