Hukumar kula da ayyukan ‘yan Sanda (PSC) ta daga mukamin Hauwa Ibrahim Jibrin zuwa matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda (CP).
An haifi Hauwa Ibrahim Jibrin a ranar 28 ga Oktoba, 1972, a karamar hukumar Fagge ta Jihar Kano, tana da digiri na farko a fannin Kimiyyar Siyasa, Digiri na biyu a fannin Tsaro da Nazarin Dabaru, a halin yanzu tana karatun Digirgir (Ph.D.).
Hauwa Ita ce mace ta farko daga Arewacin Najeriya da aka nada a matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda.
Kafin daga mukamin ta, Jibrin ta rike matsayin mataimakiyar kwamishinan ‘yan sanda a hukumar ‘yan sanda ta tarayya (FCT).
Hauwa Ibrahim Jibrin ta zama mace ta farko daga Kano da ta samu mukamin kwamishinan ‘Yan Sanda