Kano: Gwamnati za ta kashe N670m wajen yakar rashin abinci mai gina jiki

11 hours ago 2

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudurinsa na yaki da rashin abinci mai gina jiki da inganta lafiyar mata da yara ta hanyar fitar da Naira miliyan 500 a matsayin kudin tallafin haɗin gwiwa da UNICEF a jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamna Yusuf ya bayyana hakan yayin kaddamar da makon lafiya na mata masu juna biyu, jarirai da yara karo na biyu, wanda aka gudanar a karamar hukumar Kumbotso.

Haka kuma, gwamnan ya sanar da ware Naira miliyan 170 don gyaran cibiyoyin kula da rashin abinci mai gina jiki da cibiyoyin bada shawarwari don yakar cututtukan da ke kashe yara tare da saukaka samun kulawar lafiya.

“Wannan gwamnati ta kuduri aniyar yaki da rashin abinci mai gina jiki da kuma hana cututtukan da ke barazana ga rayuwar ‘ya’yanmu.

“Ta hanyar fitar da wadannan kudade, muna ɗaukar mataki mai ƙarfi wajen tabbatar da makoma mai kyau da lafiya ga ‘ya’yanmu da iyalai,” in ji gwamna.

Ana gudanar da muhimman ayyuka a makon lafiya na MNCH da ake gudanar a jihar Kano.

Kano: Gwamnati za ta kashe N670m wajen yakar rashin abinci mai gina jiki

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.