Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da damar bikin Kirsimeti wajen yin addu’a ga kasa, don samun nasarar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kawo ci gaba da wadata a Najeriya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ismaila Uba-Misilli, Darakta-janar na harkokin yada labarai na gidan gwamnati, ya fitar a ranar Talata, domin taya mabiya addinin Kirista murnar bikin Kirsimeti na bana.
Yahaya ya bayyana cewa bikin Kirsimeti wata dama ce ta musamman ga mabiya addinin Kirista su yi addu’a don ci gaban kasa da kuma magance matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta.
Ya ce manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu sun nufi gina kasa mai dorewa da wadata.
“Ina kira ga yin addu’a don ci gaba da jin daɗin al’umma, musamman a wannan lokaci na ƙalubalen tattalin arziki.
“Ina tunatar da dukkan ‘yan kasa da su kasance masu fata mai kyau da kuma ci gaba da mara wa manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu baya, wanda ke da nufin gina kasa mai dorewa da wadata ga kowa da kowa.
“Duk da cewa wadannan lokuta suna da matuƙar wahala, ina ƙarfafa mutane kada su rasa fata, amma su kasance masu kyakkyawan tunani da sadaukarwa ga hangen nesan samun Najeriya mai kyau.”
Kirsimeti: A yi wa kasa addu’o’i – Gwamnan Gombe ga Kiristoci