Kungiyar shugabannin kananan hukumomin ta kasa ALGON ta bayyana cewa kuɗaɗen da aka ware musu a kasafin kudin badi ba za su ishe su ko da biyan albashi mafi ƙaranci ba.
Sakataren kungiyar na kasa Hamisu Anani ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da BBC,inda kuma ya ce har yanzu kananan hukumomin ba su fara ganin kudaden su ba duk da hukuncin da kotun kolin kasar nan tayi.
A kasafin kudin wannan shekara an warewa kananan hukumomin kimanin naira Tiriliyan 2.
Tun bayan da kotun ƙolin Kasar nan ta yanke hukunci game da ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai-tsaye daga asussun gwamnatin tarayya, ake ta sa ran ganin alfanun da hakan zai haifar, musamman ga mutanen karkara da suka fi zama kusa da ƙananan hukumomin.
Kuɗin da aka ware mana ba za su isa biyan albashi ba – ALGON