Najeriya ta fice daga cikin sunayen kasashe Afrika goma da akafi bin bashi – IMF

17 hours ago 2

Wani sabon rahoto da asusun bayar da lamuni ta Duniya (IMF) ta fitar ya nuna Najeriya bata cikin ƙasashen Afrika da aka fi bi bashi a shekarar 2024.

Rahoton ya nuna cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekarar, gwamnatin tarayya ta biya sama da Dala biliyan 2.24 na basussukan da ake bin ta wanda ya fitar da ita daga ƙasashen da bashi ya yi musu katutu.

Rahoton da ofishin kula da basussuka na Nijeriya ya fitar ya nuna cewa a watanni 3 na farkon 2024, gwamnatin ta biya dala biliyan 1.12 na bashin da ake bin ta.

A watanni 6 na shekarar ne kuma ta sake biyan Dala biliyan 1.12 ga ƙasashe da kuma hukumomin da ke bin ta bashi da suka haɗa da IMF da Babban Bankin Duniya.

Rahoton ya bayyana ƙasar Misira a matsayin wacce take da mafi girman kaso a Nahiyar da ya zarce Dala biliyan 9.

Najeriya ta fice daga cikin sunayen kasashe Afrika goma da akafi bin bashi – IMF

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.