NDLEA ta kama mutum 34 da miyagun kwayoyi, makamai a Kano

11 hours ago 2

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta kama mutane 34 da zargin mallakar miyagun kwayoyi a jihar.

Kakakin hukumar, ASN Sadiq Muhammad-Maigatari, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Muhammad-Maigatari ya nakalto kwamandan hukumar na jihar, Malam Abubakar Idris-Ahmad, yana cewa an yi kamen ne yayin wani samame da aka gudanar, a matsayin matakin kariya don kawar da kwayoyi ba a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

“A ranar 24 ga Disamba, hukumar ta dira a wuraren hada-hadar miyagun kwayoyi da dama a fadin jihar. Wadannan wurare sun hada da yankin Fagge, Filin Wasan Sani Abacha, Dan agundi, da kuma sanannen dabar nan ta Filin Idi.”

Ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kwace muggan kwayoyi masu yawa irin su tabar wiwi, sukudayin da Exol-5, da sauransu.

Sauran kayayyakin da aka kwace sun haɗa da makamai da ake amfani da su wajen fatattakar jami’an tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a taimakawa wadanda aka samu da ta’ammali da miyagun kwayoyi kulawar da ta dace don rabuwa da muguwar ɗabi’ar.

Kwamandan ya ce wannan kamen ya nuna ƙudirin hukumar na rusa cibiyoyin hada-hadar kwayoyi da kuma rage yawaitar muggan kwayoyi a cikin al’umma yayin bukukuwan nan.

Ya kara da cewa ana ci gaba da bincike, kuma duk wadanda aka samu da laifi za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

NDLEA ta kama mutum 34 da miyagun kwayoyi, makamai a Kano

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.