Asusun Lamuni Na Ilimi a Najeriya (NELFUND) ya bayyana shirin sake duba dokokinsa game da bayar da rance mara ruwa ga ɗalibai, tare da yiwuwar cire wasu kwasa-kwasai daga cancantar samun wannan tallafin.
Babban daraktan NELFUND, Akintunde Sawyerr, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron yanar gizo da The Renewed Hope Global ta shirya.
Sawyerr ya ce asusun yana son mai da hankali kan kwasa-kwasai da suka dace da buƙatun ci gaban ƙasa, musamman waɗanda ke da kyakkyawar dama ta samar da aikin yi yanda zasu iya biyan rance cikin sauƙi.
A cewarsa, duk da cewa a halin yanzu suna bada rancen ga duk kwasa-kwasai akwai yiwuwar shirin zai sauya don fifita waɗanda za su taimaka wa cigaban ƙasa kai tsaye.
“Yanzu haka, muna kula da duk kwasa-kwasai, musamman ga ɗaliban da suke shekararsu ta uku da ta huɗu ta karatu amma mun gane cewa wasu fannoni sun fi muhimmanci wajen ciyar da ƙasa gaba.”
Ya kara da cewa, duk da cewa kwasa-kwasai kamar koyon harsuna suna da amfani, ba su da alaƙa kai tsaye da buƙatun ci gaban Najeriya na yanzu, kamar injiniyanci ko likitanci. Har ila yau, ya ce kwasa-kwasai da ke bayar da ƙwarewa da za a iya amfani da ita a ƙetare za su ci gaba da samun tallafi.
Ya zuwa yanzu, ɗalibai 335,000 daga manyan makarantu 127 a fadin ƙasar sunci gajiyar shirin.