Nijar na son tunzura Arewacin Najeriya ta tsani Tinubu – Bwala

16 hours ago 4

Mai bai wa Shugaban kasa shawara a kan harkokin sadarwa da tsare-tsare, Daniel Bwala, ya musanta zargin da Shugaban sojojin jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na hada kai da Faransa don tayar da hankali a Nijar.

Bwala ya bayyana wadannan zarge-zarge a matsayin shirin yada farfaganda, wanda aka tsara domin haddasa rikici da tada kiyayya a Arewacin Najeriya kan Shugaba Tinubu.

“Zaben harshe da Shugaban Sojojin Nijar ya yi ya nuna abin da ya ke nufi, watakila tare da wasu ‘yan siyasa a Najeriya, ba za ka sani ba, amma duk manufar ita ce haifar da rikici da tada kiyayya a Arewacin Najeriya kan Shugaban Kasa,” in ji Bwala a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a.

Bwala ya soki kalaman Janar Tchiani, inda ya ce hakan wani yunƙuri ne don karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin mulkinsa.

“Lokacin jin dadi ya ƙare; bai samu damar magance matsalar tattalin arzikin ƙasarsa ba. Duk abin da ke faruwa ya fara juya masa baya, kuma a cikin yunƙurin neman mafita, ya yanke shawarar yin ƙarya da farfaganda kan Najeriya,” in ji shi.

Bwala ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin Tchiani, yana mai cewa ba gaskiya ba ne kuma yana nufin raba kawunan mutane.

A ƙarshe, Bwala ya bayyana kalaman Tchiani a matsayin alamar gazawar mulkinsa wajen gudanar da shugabanci mai nagarta.

Gwamnatin tarayya, ta hannun Ministan Bayanai da Shirye-shiryen Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, tun da farko ta musanta zargin da Shugaban Sojojin Nijar ya yi.

Nijar na son tunzura Arewacin Najeriya ta tsani Tinubu – Bwala

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.