Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ya musanta rahotannin da ke cewa an rufe matatar mai ta Fatakwal da aka farfado da ita, yana mai cewa matatar tana aiki yadda ya kamata.
Kamfanin ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olufemi Soneye, ya fitar ranar Asabar.
A cewar sanarwar, tsofaffin shugabannin ƙungiyar NNPC sun tabbatar da matatar ta na aiki, kuma ana sarrafa ganga 60,000 a kowace rana.
“Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ya lura da rahotannin da wani ɓangare na kafofin yada labarai suka wallafa suna ikirarin cewa matatar Fatakwal da ta dawo aiki watanni biyu da suka gabata ta lalace.
“Ana ci gaba da shirin lodin samfuran man fetur na yau,” in ji sanarwar.
Sai dai NNPCL ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da irin waɗannan rahotannin, tana bayyana su a matsayin “ƙirƙirarren labari daga masu son haifar da ƙarancin man fetur na bogi don cutar da al’umma.”