Ribadu ya musanta zargin hadin baki da Faransa don tayar da hankula a Nijar

15 hours ago 2

Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya musanta zargin da shugaban sojin Nijar, Janar Abdulrahman Tchiani, ya yi cewa Najeriya tana hada kai da Faransa domin tayar da hankula a Nijar.

Janar Tchiani ya yi ikirarin cewa Najeriya ta kafa sansanin sojin faransa a tsakanin Monguno da Baga a jihar Borno.

Da yake hira da kafar BBC Hausa, Ribadu ya musanta wadannan zarge-zargen, yana mai bayyana su a matsayin marasa tushe.

Ya ce, “Ko lokacin da Ingila ta mulki Najeriya, ba ta taba girke sojoji a nan ba. Lokacin da Faransa ta nemi kawo sojojinta, mun ki amincewa. Me zai sa mu amince yanzu?”

Ya yi kira ga shugabannin Nijar da su fuskanci rikicinsu da Faransa kai tsaye ba tare da shigar da Najeriya cikin lamarin ba.

Ribadu ya jaddada cewa Najeriya tana fifita zaman lafiya da hadin kai a yankin fiye da tsoma baki a lamuran wasu kasashen waje.

Har ila yau, Janar Tchiani ya kara zargin cewa Najeriya ta ba wa sojojin Faransa wurin zama a kusa da tafkin Chadi tare da kafa sansanonin horar da mayaka a jihohin Sakkwato, Zamfara, da Kebbi.

Ribadu ya musanta zargin hadin baki da Faransa don tayar da hankula a Nijar

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.