Sabbin jagorin Siriya da suka kifar da Bashar al-Assad bayan share shekaru 13 suna kai ruwa rana da shi, sun ce a shirye suke su ba da gudummowa wajen dawo da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya tare kuma da buda kofofin kasar ga kasashe masu manufofin ci gaba a yankin.
Sabbin mahukuntan Siriya sun bayyana hakan a cikin sanarwar da suka fidda bayan kammala ganawar farko tsakannin shugaban wuccin gadi Hayat Tahrir al-Sham da wata tawagar manzannin Amurka da ta yi tattaki har zuwa birnin Damascus.
Jim kadan bayan ganawar, ofishin jakadancin Amurka ya fidda sanarwar cewa Washington ta janye tukwicin da ta saka a baya ga duk wanda ya kamo mata sabon shugaban na Siriya Hayat Tahrir al-Sham a lokacin da ya ke gwagwarma a kungiyar ‘yan ta’adda ta IS.
Sanarwar ta kuma bukaci sabbin jagororin da su gudanar da mulkin rikon kwarya cikin gaskiya da adalci wanda ya dace da ‘yan Siriya tare kuma da kiyaye tsokanar makwabta.
Sabbin jagororin Siriya sunce zasu dawo sa zaman lafiya gabas ta tsakiya