Shugaban gwamnatin Sojin Nijer ya zargi Najeriya da tallafawa turawan faransa

13 hours ago 3

Shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya zargi Faransa da ba da tallafin kuɗi ga hukumomin Najeriya don kafa sansanin soji a jihar Borno.

Tiani ya ce an shirya wannan mataki ne domin kawo rashin zaman lafiya a Nijar da ƙasashen makwabtanta.

Shugaban gwamnatin sojin Nijar ya yi wannan ikirari a wani jawabi da ya yi kwanan nan a gidan talabijin din kasar, inda ya zargi Faransa da yin katsalandan a yankin domin cimma wani mummunan nufi.

“Faransa ta yi alƙawarin bayar da kuɗi ga hukumomin Najeriya don kafa sansani a jihar Borno, domin kawai tada hankali a ƙasashenmu.

“Muna sanar da hukumomin Najeriya, ciki har da Nuhu Ribadu da Ahmed Abubakar Rufa’i, game da babbar makarkashiya ta kawo rashin zaman lafiya a Nijar.

“Daji na Gaba, wanda yake a iyaka tsakanin Sokoto (Najeriya) da Nijar, an zaɓe shi a matsayin mafaka ga ‘yan ta’adda da Faransa da ISWAP suka dauka aiki.

“Abin takaici, alamu sun nuna mun yi kuskuren zaɓar waɗanda za mu yi hulɗa da su, domin ƙwarewarsu ita ce aka yi amfani da ita wajen yin yunƙurin tayar da hankali a kan iyakokin Nijar, Najeriya, Benin da Burkina Faso,” in ji Janar Tiani

Zagazola Makama kwararre kan sha’anin tsaro a tafkin Chadi ya ce wannan zargi yana cikin jerin zarge-zargen da gwamnatin sojin Nijar ke yi wa Faransa tun bayan juyin mulkin watan Yulin 2023.

Ya ce gwamnatin Tiani tana ci gaba da zargin Faransa da yin katsalandan a harkokin cikin gida na Nijar da kuma goyon bayan ɓangarori da ke adawa da gwamnatin mulkin sojin.

A nazarinsa, Makama ya bayyana cewa zargin da Janar Tiani ya fi kama da hasashe fiye da tabbacin gaskiya.

Ya ce, “Waɗannan zarge-zargen suna kama da wata dabara don ware Najeriya saboda dangantakarta mai ƙarfi da Faransa.”

Makama ya yi gargadin cewa irin waɗannan zarge-zarge marasa tushe da aka ci gaba da yi wa Najeriya na iya zama barazana ga dangantakar diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

“Zargin da Janar Tiani ke yi ba kawai yana lalata waɗannan muhimman ayyuka ba ne, har ma yana kawo haɗarin tayar da hankalin da ba a buƙata tsakanin ƙasashen da ke da buri ɗaya na samun zaman lafiya a yankin Sahel,” ya ƙara da cewa.

Shugaban gwamnatin Sojin Nijer ya zargi Najeriya da tallafawa turawan faransa

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.