Wata motar haya da ta kwace, ta kutsa cikim masu bikin kirsimeti a jihar Gombe

12 hours ago 2

An sami rudani a jihar Gombe a ranar Kirsimeti yayin da wani direban motar haya da ya kasa sarrafa motarsa ya buge wasu masu bikin Kirsimeti.

DAILY POST sun rawaito cewa masu bikin Kirsimeti din suna cikin wani jerin gwano daga unguwar Tumfure zuwa gidan gwamnatin jihar da fadar Sarkin Gombe don kai ziyara, lokacin da lamarin ya faru.

Mutane kimanin 22 daga cikin masu bikin Kirsimeti din sun jikkata a hatsarin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, da ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na tarayya dake Gombe da kuma Asibitin Kwararru don samun kulawa.

Sai dai, Abdullahi ya ce kawo yanzu babu wanda ya rasa ransa al’amarin.

Wata motar haya da ta kwace, ta kutsa cikim masu bikin kirsimeti a jihar Gombe

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.