Shahararren mawakin Amurka, Wiz Khalifa, ya bayyana dalilin da ya sa yayi imanin cewa ya kamata masoya suyi soyayya na tsawon shekaru 10 kafin su yi aure.
A cewarsa, wannan tsawon lokaci zai bawa masoyan damar sanin halayen juna sosai kafin su ɗauki matakin aure.
A wata hira da aka yi da shi a shirin “Club Shay Shay” podcast, Wiz ya ce, “Ya kamata mutane su yi soyayya na tsawon shekaru 10 kafin su yi aure domin wannan lokaci ya isa a san mutum, iyalinsa,”
Da aka tambaye shi ko ya kamata masoya su tare kafin aure, ya ce: “Ya danganta da yanayi da kuma halin da ake ciki. Wasu mutane na tarewa nan take kuma har yanzu suna buƙatar lokaci don fahimtar juna.”
Wiz Khalifa yayi aure da samfuriyar Amber Rose a ranar 8 ga Yuli, 2013, kuma sun haifi ɗa tare a wannan shekarar.
A watan Satumba na 2014, Amber ta nemi saki, inda ta ambaci rashin jituwa a matsayin dalili.
Auren nasu ya ƙare a hukumance a shekarar 2016.
A halin yanzu, Wiz yana soyayya da budurwarsa ta tsawon shekaru biyar, Aimee Aguilar, kuma sun haifi diya tare kwanan nan.
Ya kamata masoya su yi soyayya tsawon shekaru 10 kafin aure – Wiz Khalifa