Yakubu Dogara yayi kakkausar suka ga shugabannin Arewa kan gaza inganta yankin

13 hours ago 2

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya yi kakkausar suka ga shugabannin Arewa saboda gazawarsu wajen bunkasa yankin duk da shafe shekaru masu yawa da suka yi suna rike madafun iko a kasar.

Dogara ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da shugabannin Kiristoci a Arewacin Najeriya a ranar Juma’a, inda ya ce yankin Arewa ya ci gaba da kasancewa cikin talauci saboda shugabannin yankin sun kasa zuba hannun jari a ayyuka masu amfanar al’umma.

A cewarsa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi ne matsalar Arewa ba, kuma ba a zo daga Kudu don cutar da mutanen yankin Arewa ba.

“Dukkanmu ‘yan Arewa ne, kuma ya kamata a fahimci cewa Shugaba Tinubu ko yankin Kudu ba su ne matsalarmu ba; ba su zo su cutar da Arewa ba.

Dukkanmu ‘yan Arewa ne, kuma ya kamata a fahimci cewa Shugaba Tinubu ko yankin Kudu ba su ne matsalarmu ba; ba su zo su cutar da Arewa ba.

“Wannan ba batu ne da za a duba ba. Wasu suna cewa mutanen Yarbawa suna samun mukamai, amma mu dubi tarihi.
Mun mulki wannan kasa tsawon shekaru sama da 40 ‘yan Arewa ke kan karagar mulki. Me muka cimma? Arewa ta ci gaba da kasancewa cikin talauci ta hannun shugabanninmu,” in ji Dogara.

Yakubu Dogara yayi kakkausar suka ga shugabannin Arewa kan gaza inganta yankin

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.