Yan sandan Kano sun kama matashin daya haddasa rikicin daba

17 hours ago 2

Rundunar ‘yan sanda anan Kano ta sanarda kama wani matashi bisa zargin kitsa rikicin da ya ɓarke tsakanin ’yan daba na Kofar Mata da matasan Zango da ya faru kwanan nan.

Matashin mai suna Kabiru Jamilu mai shekara 21, mazaunin rukunin gidaje na Zango Quarters an kamashi ne Unguwar Kofar Mata kusa da Asibitin kwararru na Murtala Mohammed.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda anan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin jagorantar faɗan da aka yi.

Kiyawa ya ci gaba da cewa, binciken ne ya kai ga kama Umar Garba mai shekara 32, mazaunin Zango, wanda aka same shi da wata doguwar wuƙa mai kaifi.

Tuni dai an miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Idan za’a iya tunawa dai rikicin daban da akayi kwanakin baya da ya janyo asarar rayuka da raunata wasu, kuma ya yi sanadin asarar kadarorin jama’a da dama a yankin.

Yan sandan Kano sun kama matashin daya haddasa rikicin daba

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.