Gwamnatin Benue ta ba da hutun mako 2

12 hours ago 1

Gwamna Hyacinth Alia na Jihar Benue ya sanar da hutun mako biyu ga ma’aikatan gwamnati a jihar domin murnar Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Hutun zai fara ne daga Talata, 24 ga Disamba, 2024, har zuwa Litinin, 6 ga Janairu, 2025.

A cikin sanarwar, gwamna Alia ya jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da ayyukan da suka zama wajibi a cikin wannan lokaci.

Ya ce wadannan ayyuka sun hada da na cibiyoyin kudi, hukumomin tsaro, asibitoci, hukumar ba da ruwan sha, kashe gobara, kamfanonin sadarwa, da masu samar da wutar lantarki.

Gwamnan ya nuna godiya ga ma’aikatan Benue bisa sadaukarwar da suka yi wajen ci gaban jihar, yana mai cewa jajircewar su ta kasance mai muhimmanci wajen aiwatar da shirye-shiryen gwamnati.

Ya karfafa wa kowa gwiwa da su yi amfani da hutun don zama tare da iyalai da abokai, tare da nuna kyawawan dabi’u na soyayya, hadin kai, da zaman lafiya.

Gwamnan ya taya mutanen Benue murnar Kirsimeti da sabuwar shekara.

Gwamnatin Benue ta ba da hutun mako 2

Read Entire Article
All trademarks and copyrights on this page are owned by their respective owners Copyright © 2024. Naijasurenews.com - All rights reserved - info@naijasurenews.com -FOR ADVERT -Whatsapp +234 9029467326 -Owned by Gimo Internet Tech.